Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya (hotuna, bidiyo)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga kasar Jordan bayan ya halarci taron magance ta’addanci.
Hakan na kunshe ne a cikin rubutu da Bahir Ahmad, hadimin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 4 ga waran Disamba.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasar ya bar gida Najeriya zuwa kasar Jordan a ranar Juma’a, 1 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Barin APC shine babban kuskure da Kwankwaso zai yi a rayuwarsa – Tsohon hadimin sa
Shugaba Buhari ya hadu da sarkin Jordan, Abdullahi II wanda ya fada masa cewa akwai bukatar hadin gwiwar yankuna domin magance barazanar duniya ta fannin ta’addanci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e
Asali: Legit.ng