Da’awar Musulunci: Kiristoci 87 sun karɓi addinin Musulunci a jihar Ondo
- Kimanin Mutane 87 ne, yan kabilar Yarbawa suka Musulunta a jihar Ondo
- Kungiyar addinin Musulunci, ACADIP ta shirya wa'azin Kwanaki biyu a Ondo
A karkashe wa’azi na kwanaki biyu da kungiyar ACADIP ta gudanar a Akure, babban birnin jihar Ondo, an samu mutane guda tamanin da bakwai da suka rungumi addinin Musulunci.
Legit.ng ta kalato wannan labari ne daga shafin yanar gizo na Kungiyar ACADIP, inda ta bayyana cewa a ranar farko mutane 13 ne suka Musulunta, yayin da a rana na biyu mutane 15 suka Musulunta, sai kuma a ranar rufe taro, mutane 57 suka shiryu.
KU KARANTA: Hukumar JAMB ta sanar da ranar da za ta fara sayar da fom din jarabawa
A yayin taron wa’azin an sha Karatu daga Malaman Musulunci akan batutuwan da suka shafi Annabi Isa, batun gicciye shi, da kuma karatu akan littafin Baibul, hakan sai ya zama sabon Ilimi ga dayawa daga cikin Kiristocin, wanda daga nan suka fara neman karin haske, har ta kai ga sun Musulunta.
Ga bidiyon nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng