Dandalin Kannywood: Ainahin tsakani na da Rahma Sadau - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi
A wani karon kuma, jaruma Nafisa Abdullahi ta fito tayi bayani dalla-dalla game da ainihin alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami.
Jarumar dai tayi wannan karin haske ne yayin wata fira da Weekly Trust jim-kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita zaune take lafiya da kowane abokin sana'ar ta.
KU KARANTA: Adam A. Zango zai fara gabatar wani kayataccen shiri
Legit.ng dai ta samu cewar da aka tambaye ta ko da gaske ne ba su ga-maciji da junan su ita da korarrar jarumar nan Rahama Sadau, sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani tsabani a tsakanin su yanzu.
Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma dukkan su suna yin aiki ne a karkashin kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace kuma suna fada da junan su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng