Yadda barayin shanu suke cin karensu ba babbaka a kauyukan jihar Zamfara (Hotuna)

Yadda barayin shanu suke cin karensu ba babbaka a kauyukan jihar Zamfara (Hotuna)

- Mutanen wadansu kauyuka da ke yankin karamar hukumar Shinkafi, da ke jihar Zamfara, sun yi kira ga gwamnati da su kawo musu dauki da karin tsaro saboda barnar da barayin shanu suke yi musu

- Sanadiyyar barayin shanun fiye da mutane arba'in sun rasa rayukan, sun kone muhallan su da dukiyar su

- Kauyukan sun hada da Mallamawa, Tungar 'Kahau, Garin Anna, da Unguwar Rini

Barnar barayin shanu a kauyuka
Barnar barayin shanu a kauyuka

Rahotanni a makonnin nan na nuna yadda barayin shanu ke addabar yankunan karkara a jihohin Zamfara da kewaye. Inda mahara kan kai farmaki da tsakar dare su kashe, kuma su kone kauyuka.

A baya dai da irin wadannan hare-hare suka yi kamari, har sai da ta kai an sauke bataliyar soji a yankin, ina kain qiftawa da bisimilla, aka daina jin duriyarsu. Ana janye sojin kuwa, sai suka dawo.

DUBA WANNAN: Sakon murya na wata mutuniyar Taraba na kara sarkakiya kan batun kisan Bilyaminu

A yanzu dai lamarin ya kai kololuwa, inda har shugaba Buhari yayi Allah-wadai da barayin, ya kuma yi alkawarin ddaukar kwakwkwaran mataki na ko-ta-kwana.

An dai san maharan suna buya a dazukan dake kewaye da yankin, amma har yanzu babu ko daya da ya zo hannu ko aka kaishi gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng