Bincike: Kasashe da dama na asarar duhun dare
- Hasken ya janyo tsuntsayen da ke safara a cikin dare sun sami sauyin dabi'a
- Hasken ya janyo bishiyu ma su fure suna lattin fito da 'ya'ya
- Masana sun yi kira ga mutane cewa in ba'a bukatar wuta za'a a iya kashewa da dare
Wani nazarin hotunan doron kasa da aka dauka da daddare daga tauraron dan Adam (ISS) ya nuna cewa hasken fitilun dan Adam na kara dallare sararin samaniya duk shekara.
A tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016, hasken fitilun waje da mutane ke bari a kunne na karuwa da fiye da kashi 2 cikin 100 duk shekara.
Masana kimiyya sun ce "asarar duhun daren" da ake samu a kasashe da dama na da illa ga "koshin lafiyar dan Adam, dabbobi da kuma tsirrai."
An wallafa sakamakon wannan binciken ne a cikin mujallar binciken kimiyya ta Science Advances.
Masanan sun yi amfani ne da bayanai daga wata na'urar tauraron dan Adam ta NASA, wadda takanas aka kera don auna walwalin hasken fitulun dare (NASA ita ce kungiyar binciken samaniya ta Amurka).
A binciken sun gano cewa canje-canjen da ake samu na karuwar haske a iya wannan tsawon shekarun ya sha bamban a tsakanin kasashe.
Binciken ya nun kasashen da suka fi haskakawa a duniya su ne Amurka da Spaniya, kuma hasken su bai sauya ba a iya tsawon lokacin binciken. Amma mafi yawan kasashe a Kudancin Amurka, Afirka da kuma Asiya na kara haskakawa.
Kasashe kalilan ne aka samu raguwar haskakawarsu, Yemen da Syria, wanda dukkansu ya nuna suna fuskantar yake-yake.
A cikin 2016 Kungiyar Likitocin Amurka ta baiyana cewa fitilar tsaro (sikyuriti layit) tana da mutukar hatsari saboda hasken ta. Sun yi kira ga mutane da su sauya zuwa shudin kwan lantarki mai fitar da mafi karancin haske ta yadda za a rage dallare muhalli.
Sinadaran jikin dan Adam masu sa barci musammam sun fi tasiri a cikin shudin haske.
Wani nazarin da aka buga a mujallar Nature kuma ya bayyana cewa hasken da mutane ke kunnawa na barazana ga barbarar furanni, don kuwa yana rage ire-iren wannan barbara da ake samu ta hanyar ƙwarin da ke karakainarsu cikin dare.
Bincike kuma Birtaniya ya nuna cewa bishiyoyin da ke yankuna masu haske wal suna lattin fito da furanni har sama da sati daya bayan wadanda suke wuraren da babu fitulun mutane.
Wani nazarin kuma ya gano cewa sanya fitulu a birane ya haddasa "gawurtaccen sauyin" dabi'a ga tsuntsayen da ke kaura cikin dare.
DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya zata kara haraji a kan taba da giya
Wasu mutum biyu da suka jagoranci binciken, Christopher Kyba daga Cibiyar Binciken Kimiyyar bankasa ta Jamus da ke Potsdam, da kuma Farfesa Kevin Gaston daga Jami'ar Exeter, sun i hira da kafar yada labarai ta BBC, inda suka ce suna kira ga mutane da su rage yawan barin fitulun da ba sa bukata da daddare don tallafawa lafiyar duniya baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:
labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng