Kwalejin koyan tukin jirgin sama dake Zariya za ta siya sabon jirgi
Rahoto dake zuwa mana ya nuna cewa Kwalejin koyan tukin jirgin sama na Najeriya NCAT dake garin Zariya, jihar Kaduna za ta siyo sabon jirgi ‘Boeing 737 Simulator’ a shekara mai zuwa.
Shugaban kwalejin Mohammed Abdulsalam ne ya tabbatar da hakan a yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a babban birnin tarayya Abuja.
Yace makarantar za ta siya wannan jirgi ne domin kara habbaka koyan tukin jirgin sama ga dalibai.
KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya kaddamar da fasa kauri a matsayin barazana ga tattalin arzikin Najeriya
Ya ce kwalejin ta biya kashi 70 cikin 100 (70%) na kudin jirgin.
Za’a siyo jirgin daga Kasar Canada ne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng