Ban taba ambaton Sheikh Dahiru Bauchi a wa'azina ba — Kabiru Gombe
- Kabiru Gombe ya ce bai taba ambaton sunan Dahiru Bauchi a cikin wa'azin sa ba
- Sheikh Haruna Gombe ya ce Dahiru Bauchi ya sha ambatar sunan sa da na mahaifin sa a lokacin da yake wa'azi
- Seketaren kungiyar Izala ya kalubalance duk wanda yake da kaset ko rikodin din da ya furta sunan Dahiru Bauchi ya yada a duniya
Sheikh Haruna Kabiru Gombe seketaren kungiyar Izala na kasa (JIBWIS), ya ce bai ta ba ambatan sunan babban mallamin darikar Tajjaniya na Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin wa’azin sa ba.
Seketaren kungiyar Izala ya bayyana haka ne a hirar da yayi da BBC Hausa a lokacin da shi da shugaban kungiyar Izala na kasa sheikh Abdullahi Bala Lau suka kai mu su ziyara a ofishin su dake birnin Landan a makon da ya gabata.
Kabiru Gombe ya ce, “Idan akwai wanda yake da wata kaset ko rikodin din wa’azin da ya taba ambatar sunan Dahiru Bauchi, ya fito ya yada shi a duniya.
“Hasali ma, shehi ke ambatar sunan mu a cikin wa’azin sa, ya sha kiran sunana da na mahaifi na a cikin wa’azin sa.
KU KARANTA : Shin da gaske ne kungiyar Izala ta karbi kudin makamai ?
“Kuma ya kira shugaban kungiyar mu karar da danganta shi da munana halayen da basu dadin kwatanta wa, “inji shi.
A kwanakin baya babban mallamin Darikar Tijjaniya na Najeriya sheikh Dahiru Usman Bauchi ya zargi shugaban kungiyar Izala da kai mata kasar Saudiyya dan yin karuwanci da sunan neman musu aikin yi
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng