Shin da gaske ne kungiyar Izala ta karbi kudin makamai?
- Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya karyata zargin da ake ma kungiyar Izala na karban kudin makmai
- Ana zargin tsohon shugaban kasar Najeriya da raba kudaden da aka ware dan sayo makamai da za a yaki yan kungiyar Boko-Haram ma kungiyoyi da kamfanoni dan neman kur'u.
Seketaren kungiyar Izala (JIBWIS) Sheikh Haruna Kabiru Gombe, ya karyata zargin da ake yi wa kungiyar na karban kudin makamai.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakane zanatwar da yayi da BBC Hausa a lokcin da shi da shugaban kungiyar Izala suka kai mu su ziyara a ofishin su dake birnin Landan.
An zargi tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonothan da raba wa kungiyoyi DA kamfanoni kudaden da aka ware dan sayo makaman da za a yaki kungiyar Boko-Haram dan neman kuri’u.
KU KARANTA : An nada tsohon shugaban tsagerun Neja delta Ateke Tom sarkin garin Okorichi a jihar Rivas
Gwamnatin Najeriya ta na cigaba da tsare Sambo Dsuki bisa zargin almundahana da rabawa wa mutane da kungiyoyi kudaden da aka ware dan sayan makamai.
Sambo Dasuki shine mai bawa tsohon shugabna kasa Goodluck Jonathan shawara a fannin tsaro kuma dan marigayi tsohon sarkin musulmi mai murabus mai alfarma Ibrahim Dasuki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng