Fa'idoji guda 7 na zubar da hawaye ga dan adam
Kamar dai yadda muka sani, hawaye ya na zuba ne daga idanuwan bil'adama da ma wadansu dabbobi ne saboda daya daga cikin dalilai guda 3.
Dalili na farko shi ne don samar da danshi ga kwayan idanu, wato hana kwayan idanuwa bushewa, wanda ta haka ne a ke iya gani da kyau baya ga kariya da ya ke ba wa kwayan idanun.
Dalili na biyu shi ne don hana kwayoyin cuta shiga cikin idanuwan. Misali, yayin da hayaki ko yaji ko kura ko kwaro ko dai wani abu da ka iya cutar da idanuwa ya tasar ma shiga ido, dai hawaye ya zuba don magance wadannan kwayoyin cuta.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa El-Rufai yace a rage ma'aikatun kananan hukumomi
Dalili na uku kuwa ba ya wuce dalilin da ya ke sananne ga kowa, wato sakamakon damuwa ko kunci ko bakin ciki ko wata azaba. Hawaye ya na zuba don yaye wannan damuwa don kuma tausasa zuciya.
Idan muka lura, wadannan dalilai da mu ka lissafo na zubar hawaye sun isa zama fa'idoji a karan kan su. Sai dai kuma mun kawo maku fa'idoji guda 7 wadanda malaman kimiyya da likoci su ka fitar.
Ga su kamar haka:
1. Yaye damuwa da bakin ciki, tausasa zuciya, rage radadin azaba
2. Samar da tausayawar al'umma ga mai zubar da hawayen.
3. Samar da lafiya da kuzarin jiki.
4. Bayar da kariya ga kwayar ido da kuma danyata/dansasa shi.
5. Hana kwayoyin cuta shiga cikin ido.
6. Samar da walwala
7. Sanya Jarirai yin barci. Sai dai kuma ba a kai ga gano idan kuka ya na sa manya yin barci ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng