Kashe-kashen Numan: Matasan Fulani sun fusatta, sunce zasu dauki mataki

Kashe-kashen Numan: Matasan Fulani sun fusatta, sunce zasu dauki mataki

- Wata kungiyar matasan Fulani tayi barazanar daukar mataki kan kisan mambobinsu a garin Numan har idan gwamnatin tarayya bata dauki mataki cikin gagagwa ba

- Kungiyar kuma tayi kira ga Shugaba Buhari ya sa baki kan dokar hana kiwo a fili da gwamnatocin Jihohin Bunuwe da Taraba suka zartar

- Kungiyar tace mambobin su basu tada fitina kamar yadda ake mata musu suna a kafafen yadda labarai

Wata kungiyar matasan Fulani mai suna Jonde Jam Fulani Youth Association of Nigeria, JAFUYAN ta dauki alkawarin daukan mataki game da kisan yan uwansu da akayi a karamar hukumar Numan da ke Jihar Adamawa har idan gwamnatin tarayya bata dauki mataki cikin gagawa ba.

Kamar yadda ya bayyana wa manema labarai a ranar Juma'a, Shugaban kungiyar ta JAFUYAN, Alhaji Saidu Maikano yace kungiyar zata kira taron kasa na masu ruwa da tsaki domin daukan mataki a kan zaluncin da ake yiwa mambobin su.

Kashe-kashen Numan: Matasan Fulani sun fusatta, sunce zasu dauki mataki
Kashe-kashen Numan: Matasan Fulani sun fusatta, sunce zasu dauki mataki

Kungiyar matasa kuma ta koka kan dokar hana kiwo a fili da gwamnonin Bunuwe da Taraba suka zartar a Jihohin su, suna kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunnen Gwamna Samuel Ortom da takwaransa na Taraba Darius Ishaku.

KU KARANTA: Na kashe jaririn kishiya na bisa kuskure ne, Inji Rabi'atu

A cewarsu, Yunwa na kashe shanun su domin mambobin su na tsoron abin da zai biyo baya idan suka fita kiwo kamar yadda suka saba.

Daga karshe kungiyar sunyi zargin cewa akwai masu niyyar ganin cewa sun kawar da kabilan Fulani daga Najeriya shi yasa ake yi musu kisan kiyashi a maimakon yadda ake bata musu suna a kafafen yadda labarai ana cewa sune ke tada fitina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164