Rundunar sojin Najeriya zata kafa sansanin horaswa a dajin Falgore
Hafsan hafsoshi kuma Shugaban rundunar dakarun tsaron Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Juma'a ya bayyana aniyar rundunar na kafa wani sansanin horas da dakarun sojin a cikin dajin Falgore dake a cikin karamar hukumar Doguwa, jihar Kano don shawo kan tabarbarewar tsaro a yankin.
Tukur Buratai ya bayyana hakan ne a yayin da kai wata ziyarar ba zata zuwa ga dakarun sojin dake daukar horo a dajin da a da yake zaman mafaka da kuma wurin buyar masu aikata laifuffuka.
KU KARANTA: Dalibi dan aji 3 a jami'a ya kashe kansa a Bauchi
Legit.ng ta samu dai cewa daga nan ne ma sai Buratai din ya bayar da tabbacin cewar tuni aka yi nisa wajen shire-shiren mayar da dajin sansanin horon ga sojojin Najeriya.
Ya kara da cewa tuni dai gwamnatin ta jihar Kano ta bayar da filin dajin ga hukumar ta tsaron kasar domin aiwatar da hakan. Daga karshe kuma sai ya kara karfafawa sojojin gwiwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng