Sarkin Kano ya zargi su babba da jaka bisa halin tabarbarewar arzikin Najeriya

Sarkin Kano ya zargi su babba da jaka bisa halin tabarbarewar arzikin Najeriya

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce bayyana Babba da jaka da rashin ilimi a matsayin manyan matsalolin da suka hana tattalin arzikin Najeriya cigaba.

Da yake magana ranar Alhamis yayin rufe wani taron kwana uku a kan tsaro, adalci da cigaban kasa, Sarki Sanusi II, ya bayyana cewar duk kasar da ma su kudin ta ba su sha wahalar neman kudi ba akwai rashin adalci a wannan kasa kamar yadda ake gani a Najeriya.

Sarkin Kano ya zargi su Babba da jaka bisa halin tabarbarewar Najeriya
Sarkin Kano ya zargi su Babba da jaka bisa halin tabarbarewar Najeriya

Sarki Sanusi ya kara da cewa "Cikin ma su kudin mu a Najeriya, mutum nawa ne cikin su za su iya nuna masana'anta ko kamfanin su? Matukar zamu ci gaba da samun irin wadannan ma su kudi to dole talakawa su kasance cikin wahala".

DUBA WANNAN: Masha Allah, Mutane 82 sun karbi Shahada a Jihar Osun ciki harda atishi mara addini

"Akwai bukatar mu gina tattalin arziki da zai zama tamkar madubi ga jama'a na wanda zai ke kara talauci ga jama'a ba. Tsarin gwamnati a Najeriya ya fi tsarin jari hujja hadari kuma matukar muna son cigaba ya zama dole mu tabbatar da adalci" inji Sarki Sanusi II.

Hakazalika Sarki Sanusi ya ce rashin ilimi na taka muhimmiyar rawa a tabarbarewar arzikin Najeriya. Ya ce "Yaran mu na fama da rashin ilimi da yunwa, ga rashin ingancin harkar lafiya. Kan mu zamu fara zarga kuma mu tambaya wacce irin al'umma muke ginawa?".

Shugaban taron ya bayyana cewar makasudin shirya taron shi ne samar da mizani, ta hanyar tattaunawa, ga manyan-manyan kalubale musamman na tsaro, daidaito, da talauci da suka hana arewacin Najeriya cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: