Bidiyo: Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Abdullahi Bala Lau sun tattauna da yan jarida a Landan

Bidiyo: Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Abdullahi Bala Lau sun tattauna da yan jarida a Landan

Wasu daga cikin Shugabanin kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatul Sunna (JIBWIS) sun kai ziyara kasar Ingila inda kuma suka ziyarci zauren kafan yada labarai na BBC Hausa domin tattaunawa a akan dalilin ziyara tasu da kuma amsa wasu tamboyoyi da al'umma ke dashi kan ayyukan kungiyar.

Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau da kuma Sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe sun ce dalilin ziyarar tasu shine sada zumunci tsakanin su da kuma kungiyar Sautus - Sunnah da ke kasar Ingila.

Bidiyo: Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Abdullahi Bala Lau sun kai ziyara zauren BBC Hausa a kasar Ingila
Bidiyo: Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Abdullahi Bala Lau sun kai ziyara zauren BBC Hausa a kasar Ingila

Bayan sada zumunci, sunce ziyarar zai basu damar musanyar dabarun da'awah da kuma yadda ake gudanar da ayyukan kungiya tunda dukkansu manufarsu itace yada addinin musulunci akan tafarkin Al-Qurani da Sunnan Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW).

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Jam'iyyar PDP na zawarcin Atiku da wadan su gwamnoni 5

Malaman sunyi tsokaci akan gina masaukin baki da Kungiyar tayi wadda yawancin mutane ke ganin bashi ne abin da ya dace ba, hazallika sunyi tsokaci akan Jami'ar musulunci da kungiyar ke kokarin kafawa a Najeriya.

Malaman har ila yau sunyi tsokaci akan rashin jituwa da ke tsakanin kungiyar Izala da kuma wasu Kungiyoyin addinin musulunci da ke Najeriya musamman kungiyar Darika da ke karkashin Jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Ga faifan Bidiyon yadda hirar ta kasance a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164