Bilyaminu ya gamu da abun da ya kamace shi don shi mayaudari ne - inji kawar Matar shi
Rahotanni sun kawo cewa daya daga cikin kawayen Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta Bilyaminu dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta mara ma kawar tata baya akan zargin da ake mata.
Bisa ga wani rubutu da kawai mai suna Maryam Aliyu ta wallafa a shafinta na Facebook ta nuna goyon bayan ta ga Sanda dari bisa dari.
Ta kuma kalubalanci mutane da su daina zargin kawar ta da aikata laifin da ake tuhumarta a kai.
Majiyarmu ta Pulse Hausa ta rahoto inda kawar wacce ake tuhuma ke cewa: “Bilyaminu Kasurgumin mayaudari ne kuma ya gamu da abun da ya kamace shi.
“Mutane na ta kumfar baki akan al'amarin Bilyaminu da Maryam ba tare da sanin gaskiyar abun da ya faru ba.
"Babu wata kwakwarar shaida mai nuna cewa ita ta aikata laifi. Abun da na sani shine shi dai kasurgumin mayaudari ne kuma a ra'ayi na ya gamu da abun da ya kamace shi.
“Idan ma Maryam ta kashe shi wanda na san ba haka bane, ai tayi dai dai domin yana yaudarar ta da bin mata ba tare da ta sani ba.
KU KARANTA KUMA: Sufeto Janar ya bukaci tura jami’an tsaro jihohin Zamfara da Adamawa
“Ni dai na tsaya a bangare mai cewa ya mutu ne a lokacin da suke rigama amma ba wai a ce ta kashe shi da hannun ta ba. Ki cigaba da juriya Maryam, Allah yana tare da ke." Kamar yadda ta wallafa a shafinta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng