Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Rahotanni sun kawo cewa Maimuna Aliyu wacce ta kasance mahaifiya ga Maryam Sanda, matashiyar da ake zargi da hallaka mijinta Bilyaminu Halliru na daga cikin jadawalin wadanda hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa k enema ruwa a jallo.

Idan zaku tuna, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya gabatar da sunan Maimuna a matsayin zabin fadar shugaban kasa na kujerar shugabancin hukumar kiyaye rashawa (ICPC). Sai dai bayyanan sunan na ta ke da wuya sai hukumomin rashawa suka yi rashin ammana da zabar nata, inda hujjoji bayyanannu suka fito ana tuhumar ta da yin sama da fadi da kudi naira miliyan 57.

A daidai lokacin da hukumar ICPC ke kokarin maka ta a kotu ne aka ji sunan ta ya bayyana zata jagoranci hukumar, lamarin da ya sanya fadar shugaban kasa ta janye sunan na ta.

Hukumar ICPC ta maka Maimuna a kotu, inda ta ke kalubalantar ta da laifuka uku wandanda ke da alaka da rashawar kudi.

Surukar marigayi Bilyaminu, maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
Surukar marigayi Bilyaminu, maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Wadannan laifukan da hukumar ke zargin Maimuna da faruwa sun auku ne a lokacin da take jagorantar kamfanin ajiya da basussuka na Aso.

Ko a watan Mayu, rahoton wani kwamitin bincike da 'yan sanda ta kafa karkashin sufritanda Taiwo Oyewale ya tuhumi Mimamuna da wawurar wadannan kudade, inda rahoton ya nemi a gurfanar da ita a gaban hukuma.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda na tuhumar matar dan tsohon shugaban PDP da kisan kai

Sai dai Maimuna tace bita da kulli ne kawai ake mata, kuma duka zargin da ake mata ba su da tushe. Ta ce wadanda ta fallasa su yayin da take Darakta a kamfanin ajiya da basussuka na Aso ne suka shirya mata makarkashiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng