Asibitin Mahaukata na Jihar Jigawa ya samu tallafin gadaje da katifu daga hukumar NPA
- Asibitin Mahaukata na Jihar Jigawa ya samu tallafin gadaje da katifu daga hukumar NPA
- Dakta Yakubu Abdulkadir babban likitan asibitin ya cewar kokarin hukumar ya yi dai-dai da manufar gwamnatin jihar na bunkasa harkar lafiya.
- Dakta Yakubu ya bayyana cewar ana yiwa asibitin gyare-gyaren domin jin dadin marasa lafiya
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa, NPA, ta bayar da gudunmawar gadaje, katifu, da zannuwan gado guda 40 ga asibitin mahaukata dake karamar Kazaure a jihar Jigawa.
Da yake karbar gudunmawar kayayyakin, Dakta Yakubu Abdulkadir, babban likitan asibitin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, yau laraba cewar kokarin hukumar ya yi dai-dai da manufar gwamnatin jihar na bunkasa harkar lafiya.
DUBA WANNAN: Jirgin ruwan sojin kasar Amurka na yaki ya kife a gabar tekun Japan
"Jama'a da dama na son taimakawa asibitin amma rashin jagoranci nagari ke hana da yawan ma su hali tallafawa asibitin. Zamu yi iya bakin kokarin mu wajen yin amfani da tallafin ta hanyar da ya dace". Inji Dakta Yakubu.
Dakta Yakubu ya bayyana cewar ana yiwa asibitin gyare-gyaren domin jin dadin marasa lafiya tare da yin kira ga ma su hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan halin jin kai na hukumar NPA.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng