Harin da aka kai wani Masallacin garin Mubi da safiyar nan ya rutsa da rayuka da dama
- Wani matashi dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wani masallaci dake garin Mubi, jihar Adamawa a safiyar yau
- Al’amarin ya afku ne da misalign karfe 5:20 na asuba, bayan sallar asuba; an rahoto cewa mutane 30 sun rasa rayukansu
- Kakakin yan sandan jihar Adamawa ya tabbatar da al’amarin inda ya bayyana cewa wadanda suka ji rauni na asibitoci daban-daban inda suke karban kulawa
Wani tashin bam ya afku a wani Masallaci dake garin Mubi, jihar Adamawa, a safiyar yau, Litinin, 21 ga watan Nuwamba, jaridar Punch ta ruwaito.
An rahoto cewa al’amarin ya afku ne a Kunu Araha, wani yanki na Arewacin Mubi, da misalin karfe 5:20 na safe.
Legit.ng ta tattaro cewa akalla sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu a bam din da matashi dan kunar bakin wake ya tayar.
KU KARANTA KUMA:
Kakakin yan sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da afkuwar al’amarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng