Tarihin rayuwar Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya na farko Alex Ekwume
- Shugaba Buhari yayi makokin rashin Alex Ekwume
- Ekwume ne Mataimakin Shugaban Kasa a 1979-83
- Gwamnatin Shugaba Buhari ta daure Alex Ekwume
An haifi Ekwume a Ranar 21 ga Watan Oktoban 1932 kuma ya cika ne a daren jiya yana mai shekaru 85 a Duniya. Ekwume ya rike Mataimakin Shugaban Kasa a lokacin Shehu Shagari yana Shugaban Kasa daga 1979 zuwa 1983 karkashin NPN.
Gwamnatin Sojin Shugaba Buhari ta tsare manyan ‘yan siyasar Kasar bayan ta hambarar da Gwamnati. Daga cikin wanda aka kama akwai Alex Ekwume wanda Gwamnatin Buhari ta biyawa kudin jinya kwanan zuwa Landan inda ya cika.
KU KARANTA: Buhari ya aikawa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan sako na murna
Marigayi Dr. Alex Ekwume yayi Digiri a fannin nazarin dabi’ar Jama’a a 1955 daga nan kuma yayi karatun zama kwararren magini a shekarar 1956. Ekwume ya kuma yi Digiri na biyu a fannin gine-gine na sha’anin birane (URP).
Har wa yau Marigayi Ekwume yana da Digiri a fannin tarihi a wata Jami’ar Landan. Ekwume bai tsaya nan ba don sai da yayi di-gir-gir a fannin shari’a a (LLB) Glasgow. Haka kuma ya tike inda yayi Digiri na 3 a Birnin na Glasgow.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng