Za a samar wa mutane na’aurar gwajin Kanjamau a gida

Za a samar wa mutane na’aurar gwajin Kanjamau a gida

- Ministar kiwon Lafiya Mista Isaac Adewale ya ce gwamnatin tarayya za ta samar wa mutanen kasar Na’urar gwajin cutar kanjamau da za su iya amfani da shi a gida

- Adewale ya ce sama da mutane miliyan 5.6m ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya

- Isaac Adewole ya ce tsoro, rashin sani, da kuma kunya yana daga cikin manyan kalubale da masu dauke da cutar kanjamau ke fuskanta

Ministar kiwon Lafiya Mista Isaac Adewale ya ce gwamnatin tarayya za ta samar wa mutanen kasar Na’urar gwajin cutar kanjamau da za su iya amfani da shi a gida ba tare da zuwa asibitin yin gwaji ba.

Minitsar ya bayyana haka ne a lokacin da kwamitin kula da yaduwar cutar kanjamau a Najeriya suka kawo mi shi sakamakon rahoton gwajin da suka yi.

Za a samar wa mutane na’aurar gwajin Kanjamau a gida
Za a samar wa mutane na’aurar gwajin Kanjamau a gida

Mista Isaac ya ce bincike ya nuna cewa sama da mutne miliyan 5.9m ke dauke cutar kanjamau a Najeriya kuma mutane miliyan 14m ke dauke da wannan cuta a duniya ba tare da sanin sub a.

KU KARANTA : Uwar gidan Ujukwu, Bianca ta tsinewa Peter Obi akan cin amanar mijinta

Mista Isaac Adewole ya ce tsoro, rashin sani, da kuma kunya yana daga cikin manyan kalubale da masu dauke da wannan cuta ke fuskanta.

Saboda haka ne gwamnatin tarayya ta sa ma’aikatar kiwon lafiya ta shigo da wannan na’ura Njeriya

“Wannan za sa mutane su gwanda ka su a cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng