Mataimakin gwamnan jiha ya canza sheka zuwa APC a jihar Kuros Ribas

Mataimakin gwamnan jiha ya canza sheka zuwa APC a jihar Kuros Ribas

Labaran da muke samu da dumin su sun bayyana cewa tsohon mataimakin gwamna a jihar Kuros Ribas dake a kudu-maso-kudancin kasar nan ta Najeriya mai suna Larry Odey ya canza sheka daga jam'iyyar sa ta PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Mista Odey da ke kuma zaman kakakin majalisar jihar har a watan Yunin shekarar 2015 ya canza shekar tasa ne tare da dumbin magoya bayan sa da suka tasar ma sama da 5,000 a ranar Lahadin da ta gabata tare kuma da tsohon shugaban jam'iyyar Mista Fidelis Egoro.

Mataimakin gwamnan jiha ya canza sheka zuwa APC a jihar Kuros Ribas
Mataimakin gwamnan jiha ya canza sheka zuwa APC a jihar Kuros Ribas

KU KARANTA: Kotu a Abuja ta daure wasu shekara 105 a kurkuku

Legit.ng ta samu kuma cewa an gudanar da taron gangamin ansar ta su ne a karamar hukumar Yala ta jihar a wata makarantar Firamare da shugaban jam'iyyar ta APC mista John Ochala ya jagoranta.

Taron siyasar dai ya cika-ya-tumbatsa yayin da ya samu halartar dumbin mutane manyan 'yan siyasa da suka hada Sanata John Owan-Enoh da ke wakiltar mazabar Kuros Ribas ta tsakiya da dai sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng