Wacece Jami’ar da ta fi kowace tsufa a Duniya
- Wannan karo mun kawo jerin Jami’o’in da su ka fi tsufa
- Jama’a da dama sun dauka a Turai a ka fara samun Jami’a
- Sai dai a Nahiyar Afrika aka fara kafa Jami’a a Tarihi
Za ku ji yadda wannan karo kuma mu ka kawo jerin Jami’o’in da su ka fi tsufa a fadin Duniya. Jami’o’i 13 da su ka fi dadewa a Duniya a tarihi dai su ne:
1. Jami’ar Kairuwana da aka kafa a shekarar 859
2. Jami’ar Perugia da aka kafa a shekarar 1308
3. Jami’ar Madrid da aka kafa a shekarar 1303
4. Jami’ar Sapienza ta Rome da aka kafa a shekarar 1293
5. Jami’ar Coimbra da aka kafa a shekarar 1290
6. Jami’ar Valladolid da aka kafa a shekarar 1241
7. Jami’ar Sienna da aka kafa a shekarar 1240
8. Jami’ar Naples da aka kafa a shekarar 1224
9. Jami’ar Padua da aka kafa a shekarar 1222
10. Jami’ar Cambridge da aka kafa a shekarar 1209
11. Jami’ar Salamanca da aka kafa a shekarar 1164
12. Jami’ar Oxford da aka kafa a shekarar 1096
13. Jami’ar Bologna da aka kafa a shekarar 859
KU KARANTA: Sojojin Kasar Zimbabwe sun ja kunnen Mugabe
Mafi yawan Jama’a sun dauka a Turai a ka fara samun Jami’a ko da cewa daga baya kasashen Turai irin su Sifen, Italiya da Ingila sun yi kaurin suna amma Jami’ar da aka fara kafawa a Duniya tana Birnin Fas a Kasar Morocco da ake kira Al-Qarawiyyin.
Fatima Al-Fihri wata Budurwa ‘Yar kasar Tunisiya ce ta fara kirkiro Jami’a a Duniya a kuma lokacin Musulmai su na tashe a Duniya kamar yadda mu ka samu wannan bayani a shafin tambayoyi da amsoshi na Quora.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng