Al’ajabi: Wannan yaro mai shekaru 14 na iya juya kanshi har baya (hotuna)
Abun al’ajabi baya taba karewa a duniya. Hakan ce ta kasance ga wannan yaro dan asalin birnin Karachi da ke kasar Pakistan inda yake iya juya kan shi ta yadda zai iya ganin abunda ke faruwa a bayan shi.
Yaron mai shekaru 14 a duniya, Muhammad Sameer ya kan yi amfani da hannun shi ne wajen juya kan na shi zuwa duk inda yake so.
Ya na burin wannan baiwa ta zame masa jari ta yadda sai samu gurbi a masana’antar shirya fina finai ta Hollywood inda ya ke fatan fitowa a wasanni masu ban tsoro wanda aka fi sani da ‘Horror’ a turance.
KU KARANTA KUMA: Za a fara karbar kudin aikin hajji a jihar Gombe
a cewar Sameer ya fara koyon yadda zai gudanar da wannan abu ne tun yana dan shekara shida a duniya, sannan kuma yace ya ga anyi hakan ne a cikin wani fim.
Ya ce ya sha mari ranar da mahaifiyar shi ta kama shi, inda kuma ta gargade shi kada ya sake yi saboda zai iya ji wa kan shi ciwo. Ya ce amma daga baya ta fuskanci cewa baiwa ce daga Allah.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng