Manyan yan siyasar Najeriya guda 8 da aka kama su na barci a lokacin taro
- Yawan aiki da rashin ba jiki hutu ya ke yan siyasa barci a wureren da bai kamata ba
- An samu hotonan yan siyasar Najeriya suna barci a lokacin taro ba tare da sanin su ba
Yawan aikace-aikace da rashin samu hutu, ya ke sa dan Adam barci a wuraren da bai kamata ba, ba tare da ya sanin ba.
Wannan shine labarin wasu yan siyasan Najeriya wanda ayyuka ya mu su yawa, ga kuma yawan shekaru
Duk da yawan shekrun su, sun ki ba matasa damar ta ka rawa a fannin siyasa.
Ga jerin sunayen manyan yan siyasan Najeriya da aka kama suna barci a lokacin taro.
KU KARANTA : Hukumar EFCC ta damke tsohon mukaddashin gwamnan jihar Taraba bisa zargin sace naira miliyan N450m
1. Gwamna Nyesome Wike: An dauki hoton gwmnan jihar Rivas Nyesome Wike yana barci a lokacin da ya halarci wata taron jam’iyyar PDP a birnin Fatakol.
2. Olusegun Obasanjo: An dauki hoton tsohon shugaban kasa Najeriya Olesegun Obasanjo yana barci a lokacin wata taro a Abuja.
3. Rochas Okorocha: An dauki hoton Gwamnan jihar Imo yana barci a lokacin da tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari su ke ganawa da wakilan Banki duniya a kasar Amurka.
4. Abdullahi Umar Ganduje: An dauki wannan hoton ganduje ne a lokacin taron ganawa da yan ksuwar India a kasar India.
5. BarnabaS Gemade: An dauki hoton Senata Bernaba Gemade mai wakilatar mazabar Arewa maso gabashn jihar Benuwe a lokacin da yake barci a cikin majalisar dattawa.
6. Babatunde Fashola : wannan hoton tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma ministar ayyuka a lokacin da yake barci a cikin bas.
7. Hon Essein Ayi : An dauki hoton wannan dan majalissar dake wakiltar mazabar kudanci Calabar/Akpabuyo da Bakassi a lokacin da shugaban kasa yake gabatar da kasafin kudin shekara 2016 a majalissa
8. Senata Godswil Akpabio : An dauki hoton senata Akpabio yana barci a cikin majalisar dattawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng