Yayan Maryam Booth yayi soyayya da ita, amma fa a fim, a cewarsa

Yayan Maryam Booth yayi soyayya da ita, amma fa a fim, a cewarsa

- Jarumai Ramadhan da Maryam Booth wa da qanwa ne

- A cewarsa an saka shi soyayya da kanwarsa a wani shirin fim

- Rayuwar jariman fin na karkashin sa idon mutane, kuma kwarewarsu ita ke sa suyi kowanne role aka basu

Jarumi Ramadhan Booth ya shaidawa manema labarai yadda role din fin ya sanya shi soyayya da kanwarsa a wani sabon fim ai suna Gwarzon Shekara.

Yayan Maryam Booth yayi soyayya da ita, amma fa a fim, a cewarsa
Yayan Maryam Booth yayi soyayya da ita, amma fa a fim, a cewarsa

Hoto daga BBC Hausa

A dai sana'ar fim a kasar Hausa, kamar a sauran kasashen duniya, duk irin shiri ko labari da aka baka dole kayi, in dai kana so ka nuna kwarewarka. A irin haka ne aka hada shi da kanwarsa a matsayin saurayi da budurwa, abu da yayi masa bambarakwai.

Shi dai Ramadhan a aske yaya ne ga Malama Maryam, kyakkyawar yarinyya 'yar kwalisa. Sun kuma fito ne daga gidan fim, tunda mahaifiyarsu ma tana yin shirin fim, haka ma kaninsu, Amude Buzu.

DUBA WANNAN: Femi Adesina ya kare zargin Buhari da bangaranci

Sai dai sa'ar guda da yaci, ba irin shirin im ne na kasashen waje maras tarbiyya ba, balle ace sai an yi wasu abubuwa da sunan soyayyar, wannan dai a fim na Hausa, sai dai rawa da waka, da shaukin juna.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng