Wata tsaleliyar budurwar ta bayyana sha'awar ta na takarar kujeran majalisa a Bauchi

Wata tsaleliyar budurwar ta bayyana sha'awar ta na takarar kujeran majalisa a Bauchi

- Wata budurwa ta bayyana shawarta na tsaya wa takarar kujeran sanata a jihar Bauchi

- Budurwar mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir har ma ta bayyana tsare-tsaren guda 9 da ta tanadar ma mutanen yankin ta idan har sun zabe ta

A halin yanzu da yan Najeriya ke shirye-shiryen fuskantar babban zaben shekarar 2018, matasa da dama na nuna sha'awarsu ta tsayawa takara a zaben.

Wannan ya biyo bayan kudirin rage shekaru na takara da Majalissar Najeriya ta rattafa hannu a kai kwanakin baya waddaya baiwa matasa masu kananan shekaru fitowa takarar.

Wata budurwa mai suna Ziyaatulhaqq Usman Tahir ta bayyana sha'awar ta na tsayawa takarar kujerar Sanata a yankin Bauchi ta kudu a zaben 2019 mai zuwa.

Kalli kyakyawar budurwar da ta fito takarar kujeran majalisa a Bauchi
Kalli kyakyawar budurwar da ta fito takarar kujeran majalisa a Bauchi

Bayan bayyana sha'awar nata ta shafin sada zumunta na Istagram, Ziyaatulhaqq ta zayyana abubuwan da zata yima al'ummar mazabar ta kamar haka:

Mazabar Bauchi ta Kudu ku fito ku zabi Ziyaatulhaqq Uman Tahir

1) Ilimi kyauta mun mun dauke wa iyayen ku

2) Zamu dauke wa iyayen yara mata kayan daki

3) Iyaye mata za'a ware masu albashin N100,000 duk wata ladan tarbiyar da suk wa yaran mu

4) Zamu han yan mata talle

5) Duk wanda yayi fyade za'ayi masa sabuwar kaciya sannan a daure shi gidan yari har tsawon shekaru 25

DUBA WANNAN: Tubarkallah! An samu haihuwa 72 cikin masu yiwa kasa hidima na shekarar 2016/17

6) Zamu aurar da zaurawa da mutunci

7) Zamu tallafwa marayu har karshen rayuwarsu

8) Zamu gyara yankin Bauchi ta Kudu

9) Zamu kauda talauci da handama, rashin ilimi da babakere

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164