Lafiya Jari: Amfani 6 na ganyen Lalo ga lafiyar dan Adam
Legit.ng cikin bankade-bankaden ta, ta yi mamakin binciko wasu sirraka da ganyen Ayoyo ya kunsa, wanda wasu kance ganyen lalo, inda yarbawa kan kira shi da Ewedu da kuma Inyamuari masu kiran shi Achingbara.
Shi dai ganyen Ayoyo ya na da arzikin sunadarai masu gina jiki da suka kunshi; protein, iron, calcium, phosphorus, potassium, fibers, vitamin A, vitamin C, vitamin E, riboflavin, niacin da kuma folate. Dukkanin wadannan sunadarai sukan yaki cututtuka da dama tare da wanzar da lafiya a jikin dan Adam.
Binciken masana kiwon lafiya da kuma na abinci ya bayyana cewa, wadannan sunadarai da suka hadar da vitamins da antioxidants masu tace amfanin abinci, su na da matukar amfani wajen gina jiki tare da bayar da kariya ga jikin dan Adam.
Legit.ng ta kawo muku jerin hanyoyin kiyaye lafiya da ganyen Ayoyi ke yi ga jikin Dan Adam.
1. Sunadaran vitamins A, C da E su na matukar bayar da kariya ga cutar daji wato kansa.
2. Ganyen Ayoyo na taimakawa ga masu san gyaran fatar jikin su wajen inganta wa tare da kawar da kara wa fatar sunadarin collagen mai habaka lafiyar ta fata.
3. Akwai sunadarin fiber mai taimakawa wajen rage nauyi da kuma tebar jiki.
4. Ganyen ya na kara inganta garkuwar jiki, ta yadda jikin dan Adam zai yaki kananun kwayoyin cututtuka daban-daban.
KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Amfani 5 na Goruba ga Lafiyar Dan Adam
5. Sakamakon sunadaran vitaminsa da minerals, ganyen ayoyo ya kan taimaka wajen warkar da ciwon ciki kamar irinsu, gudawa, kwarnafi da tashin zuciya.
6. Akwa kuma sunadarin beta-carotene kunshe a cikin ganyen ayoyo, wanda ke taimakawa wajen inganta karfin gani da lafiyar idanu.
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng