Wani Bawan Allah ya dauki nauyin kula da matar da ta haifi ‘Yan 4
- Wata Baiwar Allah ta haifi Yara ‘Yan 4 a Jihar Katsina
- Wani Dan siyasa dai ya tallafawa Matar da kayan yara
- Sagir Malumfashi ya dauki dawainiyar suna da sauran su
Kun ji cewa a farkon wannan makon wata Baiwar Allah ta zubo yara ‘yan 4 a Garin Malumfashi da ke Kudancin Jihar Katsina kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar nan ta Mikiya.
Tuni dai wani na kusa da mai girma Gwamnan Jihar Katsina Mai Girma Aminu Bello Masari watau Injiniya Muntari Sagir ya dauki nauyin kayan suna da na dawainiyar wadannan jarirai. Muntari Sagir Malumfashi ya taimakawa Matar da kaya.
KU KARANTA: Malamai za su koma yajin aiki a Najeriya?
Sagir Malumfashi ya kai wa Matar data haifi yan hudun tallafi a Unguwar Gora na Garin na sa na Malumfashi a Ranar Talatar nan. Wannan mata ta haifi maza uku ne dai da kuma mace daya a lokaci guda a babban Asibitin Garin na Kwandala.
Injiniya Sagir Malumfashi ya dauki dauyin ragon suna da kuma kayan abincin yaran wannan mutumi mai suna Malam Zubairu. Honarabul din ya ba Mahaifiyar yaran turamen atamfa tare da kudin kashewa. Sai dai an yi wannan mata addu’a don kuwa sai dai aka yi mata aiki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng