Abin mamaki bai karewa! 'Yan mata a Borno sun roki Gwamnatin Jihar ta aurar da su
- Alhaji Bukar, wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook ne ya bayyana hakan
- 'Yammatan wadanda tuni su ka isa aure, sun roki Gwamnatin Jihar ta su ta aurar da su kamar yadda Gwamnatin Jihar Kano ta yi
Wani Alhaji Bukar ya saka hoton wasu tuzurai mata guda 3 a inda ya yi ikirarin su na rokon Gwamnan Jihar su ta Borno wato Kashim Shettima da ya taimaka ya samo masu mazajen aure.
Su dai wadannan 'yammatan 'yan asalin Jihar ta Borno ne a wani gunduma na babban birnin Jihar wato Maiduguri.
A cewar su, su na so a tallafa masu kamar yadda Gwamnatin Jihar Kano ta tallafawa 'yan uwan su mata ta hanyar samo masu mazaje da daukan dawainiyar auren na su.
DUBA WANNAN: Hotuna: Osinbajo ya wakilci shugaba Buhari wajen tsayar da dan takarar gwamna a Anambra
Legit.ng ta na mai tunashe ku yadda akalla aure 5000 Gwamnatin Jihar kano ta gudanar a tallafin aure da Gwamnatin Kwankwaso ta faro a shekarar 2012.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng