Ban yi nufin kunyata Atiku Abubakar ba, in ji tsohuwar surukar sa

Ban yi nufin kunyata Atiku Abubakar ba, in ji tsohuwar surukar sa

- Tsohuwar surukar Atiku Abubakar, Ummi Bukar Bolori, ta ce ba ta da nufin kunyata Atiku

- Ta yi wannan bayani ne saboda rigimar su ta kula da 'ya'ya tsakanin ta da tsohon mijin nata Aminu

- Ta ce tsohuwar sarakuwar ta Titi ce silar rigimar kuma tsohon mijin na ta ya yi mata tinkahon babu wanda ya isa ya ja da su

Ummi Bukar Bolori, Tsohuwar matar dan Atiku Abubakar wato Aminu, ta yi bayani dalla-dalla a kan abun da ya janyo rigimar su na neman izinin ganin 'ya'yan su, Amirah da Aminu.

Ummi ta bayyana wa Jaridar Punch yadda har sau biyu ta na neman sasantawa ta hannun Atiku cikin ladabi da 'ya take yi wa mahaifin ta. Ta ce ta na tunanin ko shi Atikun ba zai goyi bayan dan sa ba bisa ga fallasar lamarin.

Ba nufi na bane in kunyata Atiku Abubakar, Inji surukar Atiku
Ba nufi na bane in kunyata Atiku Abubakar, Inji surukar Atiku

A cewar ta, ta bi duk wata hanyar lumana da sirri da ya kamata ta bi amma lamarin ya ci tura. Ta ce ba a son ran ta bane ake cikin halin da ake yanzun.

DUBA WANNAN: Dan kunan baikin wake Abdulmutallab ya kai karar Ma'aikatar Shari'ar Amurka

Ummi ta zargi matar Atiku, Titi, da fallasawa al'umma halin da a ke ciki ta hanyar hana ta kasancewa tare da 'ya'yan nata. Ta ce shi tsohon mijin nata da kan sa ya fada mata uwar sa ce ta umurce shi da ya hana ta ganin 'ya'yan nata.

Ta ce har fada mata ya yi cewan babu wanda ya isa ya ja da su. A cewar ta, akwai ma wani lokaci da Titi ta fada wa DPO ya kama ta saboda ta je ganin 'ya'yan nata a makaranta. Ta kuma ce Titi na mata hakan ne saboda jin zafin rabuwa da dan ta da ta yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164