Wani Yaro mai shekaru 11 ya baje kolin basirarsa ne ƙere-ƙere a jihar Kebbi (Hotuna)
Sau tari ana samun yara maza da mata daga nahiyar Afirka, musamman a Arewacin Najeriya masu hazaka da fasaha, inda ake ganin da za’a tallafa musu da sun baiwa Duniya mamaki.
A nan ma wani karamin Yaro aka samu wanda shekarunsa basu wuce goma sha daya ba, wanda ya baiwa jama’a da dama mamaki da irin basirarsa wajen kere-kere, kamar yadda Rariya ta ruwaito.
KU KARANTA: Abin kunya: Shugaban kwalejin kiwon lafiya na jigawa da Daraktan kwalejin sun dambace akan N6,000
Wannan Yaron mai suna Abubakar Suleiman dalibi ne a makarantar Sakandari ta Sojoji dake garin Jega, kuma ya shahara wajen kera abubuwa da dama, inda yake amfani da kwalaye, robobi, gwangwani da sauransu.
Daga cikin abubuwan da yaron ke kerawa, akwai babbar motar haka kasa, motar aikin noma da kuma motar kwasan kasan kan ta, abin mamakin a nan shine dukkanin abubuwan da yaron nay a kera suna tafiya da kansu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abubakar ya kan yi amfani ne da batira da wasu na’urori da zasu tura mototin gwangwanin nasa, don su dinga tafiya, wanda hakan ne ya baiwa jama’a mamakin basirar Abubakar a yan shekarun dayake dasu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli Legit.ng TV
Asali: Legit.ng