Sabuwar doka ga Musulman duniya, Sarkin Saudiyya zai sanya doka kan amfani da tantance hadisai

Sabuwar doka ga Musulman duniya, Sarkin Saudiyya zai sanya doka kan amfani da tantance hadisai

A shekarun nan an sami kungiyoyi daban-daban da ke tutiya da addinin Islama suna kashe mutane da sunan addinin da jihadi, suna yanko ayoyi da hadisai domin cimma manufarsu. Koda yake musulmi duk bassu da damar chanza Qur'ani, suna da damar ajje ko kin yin aiki da hadisai, musamman in ba'a yarda da ingancinsu ba.

Yanzu dai Saudiyya karkashin mulkin Sarki Salman tace za'a fara tantance wadanne irin hadisai 'yan ta'adda ke amfani dasu domin jihadi da yada barna. Kungiyoyi kamar Boko Haram, Al-Shabab, da Al-Qaida, da ma ISIS, da Islamic Jihad da Hamas, da Abu Sayyaf, da Taliban, da Lashkar E Taiba, dai duk daga addinin na Islama bangaren izala suka sami hujjojin yake-yakensu.

Sabuwar doka ga Musulman duniya, Sarkin Saudiyya zai sanya doka kan amfani da tantance hadisai
Sabuwar doka ga Musulman duniya, Sarkin Saudiyya zai sanya doka kan amfani da tantance hadisai

Su kuma Hezbolla da sauran 'yan shia masu tada kayar baya, sun bullo ne daga kasar Iran. Duk dai wadannan kungiyoyi suna tutiya da addini na Islama ne, koda yake su sauran musulmi sunce addinin nasu na zaman lafiya ne.

Yanzu dai, sanarwar da ta fito daga masarautar, tace Sarkin ya kafa kwamitin malamai da zasu zauna su tantance yadda ake yada hadisan, da ingancinsu, domin tsayar da ta'addanci da sunan addinin Islama. Kwamitin a birnin Madina zayyi aiki.

Tun ziyarar da shugaban Amurka ya kai kasar dai ya yi kira da Saudiyyar tayi hobbasa kan yaki da ta'addanci, inda kasar ta fara da janye wasu litattafai da ake karantarwa a masallatai na duniya, da ma kakabawa kasar Qatar takunkumai a matsayin kasa mai yada akidar ta'addanci, da azurta su.

DUBA WANNAN: Hwanarabul Gudaji Kazaure yace a bar jama'a suyi ta hayayyafa a arewa, koda kuwa ana talauci da almajirci da ta'addanci

Wani kalubale da shirin zai fuskanta, shine, ko su 'yan ta'addar zasu ajje makamansu su bi sabuwar fahimtar, ko kuwa, kamar yadda suke cewa, masarautar kanta ba halastacciya bace, domin khilafa annabi ya bari ba mulukiyya ba.

Koma dai menene, wannan zai hana sabbin samari da ke daukar karatu a masallatai da Saudiyyar kan aikowa kudi da tallafi, zamiya su fada mummunar fahimta da zafafa ra'ayi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng