Allah ya yi wa mahaifiya shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala rasuwa
- Kungiyar Izala tayi rashi na mahaifiyar daya daga cikin manyan malamanta
- Anyi jana’izarta daidai da koyarwar addinin musulunci a garin Jos
Kungiyar Izala tayi rashi na mahaifiyar daya daga cikin manyan malamanta wanda ya kuma kasance kusa a wannan kungiya.
Allah ya yi wa Hajiya Inna rasuwa wacce ta kasance mahaifiya ga Ash-sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus Sunnah.
An kuma yi jana'izar ta kamar yarda addinin musulunci ya tanadar a garin Jos, babban birnin jihar Plateau.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya kuduri aniyar inganta rayuwar ‘yan Niger Delta
Allah ya ji kanta ya kyautata makwanci, ya ba al'ummar musulumai hakurin rashinta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng