Rahama Sadau ta yi zarra: Tashin farko, Rariya ya kere ma Mansoor, Dan Kuka da Zinaru a masana’antar Kannywood

Rahama Sadau ta yi zarra: Tashin farko, Rariya ya kere ma Mansoor, Dan Kuka da Zinaru a masana’antar Kannywood

Fitacciyar jarumar Fim din nan da aka sallama daga Kannywood, Rahama Sadau ta kafa tarihi, inda tashin farko, Fim din yayi suna tare da karbuwa a masana’antar Kannywood.

Jaridar Pulse ta ruwaito Fim din na Rariya ya kayatar da yan kallo sosai da sosai, har ma ya tsere ma manyan Finai finai da aka fitar a wanann shekara kamar su ‘Yar Fim’, ‘Mansoor’, Dan kuka’ da Zinaru.

KU KARANTA: Ýan ƙasa Nagari dake amfana da shirin N-Power sun bada agajin kujeru da tebura ga makarantar Firamari (Hotuna)

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Fim din na Rariya an gabatar da shi ne a ranar 26 ga watan Yunin bana, inda aka kalle shi a garuruwan Abuja da Kano, hakan yasa yan kallo suka dinga shaukin fitarsa gaba daya.

Rahama Sadau ta yi zarra: Tashin farko, Rariya ya kere ma Mansoor, Dan Kuka da Zinaru a masana’antar Kannywood
Hoton

Shi dai Fim din Rariya ya kunshi jarumai kamar su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Hafsat Idris, Fati Washa, Maryam Booth da sauransu, sa’annnan Yaseen Auwal ne ya bada umarnin.

An shirya Fim din ne da nufin fadakar da al’umma kan sauyin da zamani ya kawo, musamman a jami’o’i, ta irin kayan da ake sawa, da kuma rayuwar karya da wasu daliban ke yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng