Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi tace ta gaji da 'yan Najeriya
Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta fada a shafin ta na sada zumunta cewa ita ta gaji da 'yan Najeriya saboda sabar sa ido da ke gare su tare da kuma maida karamar magana ta zama babba.
Jarumar dai da yi wannan rubutu ne a shafin nata inda take nuna rashin jin dadin ta game da yadda wasu 'yan Najeriya ba su da wani aikin yi sai dai su zauna suyi ta ruruta maganar da bata kai ta kawo ba.
KU KARANTA: Soyayya ce ta sa ni na fara yin waka - Umar M. Shareef
Legit.ng ta samu dai jarumar haka ma dai bada shawarar cewa kamata yayi mutum yayi kokari ya gyara nasa kuskuren ba wai yayi ta ruruta na wani ba kamr shi baya yi.
Ga dai gundarin abun da jarumar ta rubuta: "Mutane da yawa ba aikin yi, shi yasa duk kankancin abu sai ya zama abun magana. Na gaji da yan Nigeria wallahi; kowa sai ya dinga yi kaman wani mutumin Allah mutumin Allah. Mutum ya yi kokari ya gyara kurakurensa, ya daina yi kaman shi waliyyi ne."
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Watch Nigerian singer Simi perform tracks from her brand new album Simisola On Legit.ng TV
Asali: Legit.ng