Shugaba Buhari ga shugaban kasar Sin - Ina farin cikin alakar dake tsakanin kasashen mu

Shugaba Buhari ga shugaban kasar Sin - Ina farin cikin alakar dake tsakanin kasashen mu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin ciki da kuma jin dadi kan yadda ake amfana matuka dangane da alakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin.

A wata wasika da shugaba Buhari ya aikawa da mai martaba shugaban al'ummar jamhuriyyar Sin Xi Jin Ping, inda yake taya shi murna wani bikin taron kasa na 19 na jam'iyyar CPC ta kasar Sin (Communist Party of China).

Legit.ng ta ruwaito daga wasikar shugaba Buhari cewa, "A madadin al'umma da gwamnatin kasar Najeriya, ina farin cikin taya ka murna tare da tawagar wakilai 2287 da kuma mambobi miliyan 80 na jam'iyyar bisa ga wannan bikin taro na 19 da jam'iyyar ta CPC ta gudanar.

Shugaba Buhari ga shugaban kasar Sin - Ina farin cikin alakar dake tsakanin kasashen mu
Shugaba Buhari ga shugaban kasar Sin - Ina farin cikin alakar dake tsakanin kasashen mu

"Ina da cikakkiyar amincewa akan wannan taro na 19 na jam'iyyar CPC cewa zai zamto muhimmi cikin tarihin kasar Sin, kuma hakan zai assasa cikar burikan jam'iyyar da kuma kasar baki daya".

"Shugabancin jam'iyyar CPC ya na assasa zumunta da hadiin kai kamar yadda tsarin kasar ya tanadar. Kasar Sin ta samu ci gaba da dama karkashin shugabancin CPC kuma hakan ya zamto abin alfahari da kwaikwayo ga kasashe ma su tasowa da kuma kasashen duniya baki daya.

KARANTA KUMA: Kungiyoyi 10 ma su karfin gaske a Najeriya

"Cikin shekaru 30 da suka gabata, fiye da al'ummar kasar Sin miliyan 700 sun fita daga cikin kangin talauci, wanda haka ya zamto kamar wata mu'ujiza a cikin tarihin kasar."

"Kamar yadda ka saba ikirari, jajircewa da kwazo wajen aiki shi ke kawo girma da daukaka. A karkashin hadin kai da gwiwar jam'iyyar CPC tare da gudanarwar shugabancin ka, jam'iyyar ta taka wani munzali da ya karfafa hadin kan kasashe, wanda a yanzu na gamsu da irin amfanuwa da alakar Najeriya da kasar Sin ta yi sanadi."

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng