Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani hari mara nasara da suka kai Maiduguri

Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani hari mara nasara da suka kai Maiduguri

An rahoto cewa yan kunar bakin wake hudu sun mutu a wani hari da suka yi yunkurin kai wa Maiduguri, jihar Borno a daren ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba.

Yan kunar bakin waken da ake zargin yan Boko Haram ne sun kasance mata sannan sun kai farmaki yankin Ummarari wajen Maiduguri sannan kuma suka dana bama-bamansu da misalign karfe 8:23 na daren jiya, Sahara Reporters sun ruwaito.

Wani idon shaida yace dukkan yan kunar bakin waken sun kasance matasa sannan kuma suna sanye da sababbin kaya domin gudun karda a kama su.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya bayyana yadda za’a cimma sake fasalin al’amuran kasa

Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani har mara nasara da suka kai Maiduguri
Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani har mara nasara da suka kai Maiduguri

“Muna bakin aiki, sai muka ji karan fashewar abu, nayi gaggawan darewa kan garu yayinda na kunna hasken toci sai na hangi mata uku tsaye a bayan shingen don haka sai na nemi doki; sai yar kunar bakin waken ta biyu ta tayar da kanta.

Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani har mara nasara da suka kai Maiduguri
Yan kunan bakin wake hudu sun mutu a wani har mara nasara da suka kai Maiduguri

“Ta ukun ma sai ta kai hari masallaci a Ummarari babu kowa a ciki, a halin yanzu hukumar bayar da agajin gaggawa sun zo sun kwashe gawawwakin yan kunan bakin waken a safiyar Alhamis."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng