Hotunan zaman majalisar zartarwa na yau da Buhari ke jagoranta a yanzu haka

Hotunan zaman majalisar zartarwa na yau da Buhari ke jagoranta a yanzu haka

A yau Laraba 11 ga watan Oktoba ne shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya samu halartar zaman majalisar zartarwa, inda ya jagoranci zaman.

Wani ma’abocin shafin sadarwa na Facebook Buhari Sallau ne ya daura hotunan zaman majalisar inda aka hangi shugaban kasa Buhari tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo tare da sakatariyar gwamnati na rikon kwarya sun halarta.

KU KARANTA: Farashin shinkafar Hausa ya sauko a kasuwannin garin Jalingo

A irin wannan zama na majalisar zartarwa ne ake tattauna batutuwan da suka shafi kasa a tsakanin shugaban kasa, da ministocinsa, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Hotunan zaman majalisar zartarwa nay au da Buhari ke jagoranta a yanzu haka
Hotunan zaman majalisar zartarwa

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince ma ma’aikatar ayyuka, lantarki da gidaje da su gina manyan hanyoyi guda 25 a dukkanin fadin kasar don saukaka ma yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta.

Hotunan zaman majalisar zartarwa na yau da Buhari ke jagoranta a yanzu haka
Buhari

Wasu daga cikin hanyoyin nan sun hada da gadar Oju/Loko-Oweto dake samar tafkin Benuwe ya isa har kauyen Loko dake Nassarawa akan farashi N144,708,134.18, kuma za’a kammala shi a watan Disambar 2017.

Hotunan zaman majalisar zartarwa na yau da Buhari ke jagoranta a yanzu haka
Osibanjo

Da kuma aikin mayar da titin Abuja-Abaji-Lokoja tagwayen hanya, akan naira biliyan 3, kuma za’a kammala shi cikin watan Maris din 2018, da kuma cigaba da mayar da titin Suleja-Minna tagwayen hanya, wanda za’a kashe masa naira 3,521,958,532,49, kuma a gama shi a watan Afrilun shekarar 2018, da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Manyan labarai na cikin satin daya gabata, kalla a Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng