Harin Mubi: Mutane 50 ne zuwa yanzu suka rasa ransu
- Mutane 50 sun rasa ran su a bam din da ya tashi a Mubi
- 'Yan sanda na kokarin gano wadanda suka ji rauni
- Yaro ne dan kunar bakin wake ya tada bam din a masallaci
Hukumar ‘yan sandan Adamawa ta ce mutanen da suka rasa ran su sakamakon bam din da dan kunar bakin wake ya tada sun kai 50.
Malam Usman Abubakar ma’aikaci a hukumar ya tabbatarwa da gidan jarida da faruwar hakan wanda ya shaida cewa wanda ya tada bam din yaro ne a lokacin da ake sallar asuba.
‘An samu mutane 50 da suka rasa ran su, a yanzu haka muna kokarin duba yawan wadanda suka sami rauni’ Malam Abubakar.
DUBA WANNAN: Zaben Anambra ya nuna an yi riba a garambawul din da aka yi a harkar zabe - Shugaba Buhari yayin da yake taya Gwamna Obiano murna
A safiyar yau ne ciyaman na karamar hukumar Mubi, Musa Bello ya ce an tabbatar da rasuwar mutane 22 a safiyar da aka kai harin.
Legit.ng ta sami rahoton tashin bam din a unguwar Dazala da ke Mu.bi da karfe 5 na safe yayin da ake gudanar da sallar asuba a masallaci
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Wannan shine karo na farko a cikin shekaru 3 tun bayan da aka yaki kungiyar ‘yan Boko Haram daga Mubi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng