Soja marmari daga nesa: Kalli horon da ake baiwa Sojojin Najeriya

Soja marmari daga nesa: Kalli horon da ake baiwa Sojojin Najeriya

Soja marmari daga nesa, Soja birgimar hankaka, kamar yadda bahaushe yake fadi. Sanannen abu ne rundunar Sojin kowace kasa nada matukar muhimmanci ga zaman lafiyar kasar.

Hakan ya sanya aikin Soji zama mashahurin aiki da mutane da dama ke sha’awar sa, musamman matasa majiya karfi, kamar yadda Legit.ng ta tabbatar.

KU KARANTA: Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

Sai dai kash ba kowa ke iya jure horon da Sojoji ke sha ba kafin su zama cikakkun Sojoji, don an sha samun labarn yadda matasa da dama ke mutuwa yayin samun wannan horo, wanda shike bambamta duk wani Soja da farar hula.

Soja marmari daga nesa: Kalli horon da ake baiwa Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya
Asali: Depositphotos

Wannan ne abin da yasa da dama daga cikin mutane ke tserewa daga sansanin da zarar sun fara karbar horo yadda ya dace.

BBC Hausa ta kawo wani bidiyo wanda ke nuna yadda ake horar da Sojojin Najeriya, kurata a sansanin horaswa dake garin Zaria, na jihar Kaduna. Kalle shi a nan.

haka zalika mun binciko wani bidiyo da aka saka a wannan shekarar, dake nuna horon da Sojoji ke samu,kamar yadda ma'abociyar facebook Adeola Fayehun ta daura: shima kalle shi a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng