Kiwon Lafiya: Hanyoyi 5 domin kare kamuwa da cutar dajin mama (Kansa)
Kansar nono ya yawaita a tsakanin mata a wannan zamani. Don haka ya na da kyau ko wace mace ta san yadda zata nisanta kan ta daga kamuwa da shi.
Mun kawo maku hanyoyi masu sauki kuma wanda malaman kiwon lafiya su ka tabbatar don kare kan ku daga kansar nono. Mun tsamo daga wallafar Chinenye Ozota a wata Mujallar Kiwon Lafiya mai suna Envogue.
Wadannan hanyoyi ba wai wani kudi ko lokaci za su ja maku ba. Hasalima aikace aikace ne da kulawa da wasunku sun riga sun saba yin su. Ga hanyoyin kamar haka:
1) Kula da Nau'in Abinci da ake ci
Ku guji cin abinci dan kanti da aka sarrafa a inji saboda ana sa mar sinadarai na hana ruba. Wadannan sinadarai suna haifar da kansa sannu a hankali. Ku kuma guji yawan cin maiko da kitse da kabohaderet. Ku lizimci cin abinci masu gina jiki da da 'ya'yan itatuwa da ganyanyaki.
2) Yawaita Motsa Jini
Ku lizimci motsa jini akai akai akalla sau 3 a ko wani mako, ko wani lokaci akalla na minti 30. Hakan yana nisanta mace daga kamuwa da cutar kansar nono da ma sauran cututtukan kansa.
3) Kula da Tsarin Rayuwa
Ku kula da tsarin rayuwar ku ta hanyar nisantar shaye-shaye ko ciye-ciye da zai sanya rayuwar ku cikin hatsari. Ku guji shan taba da shan giya.
DUBA WANNAN: Abun mamaki: Wani gari da maza ke shigar mata
4) Kula da kayan Kwalliya na shafawa
Ku guji yawan yin amfani da kayan shafe-shafe masu dauke da sana'antattun sinadarai. Wadannan sinadarai su na iya yanjo ma mace kamuwa da kansa bayan wani lokaci.
5) Kula da yanayin canji a jiki
Ku kula kuma ku sa ido akan abun da ke faruwa a jikin ku. Da kun ga wani canji ko wani abu da ba ku gane masa ba, ku hanzarta wurin likita don ya duba ku.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng