Magungunan da fatar Jaki ke yi ga wasu cututtuka da suka addabi dan Adam

Magungunan da fatar Jaki ke yi ga wasu cututtuka da suka addabi dan Adam

A she kowa na da rana, har da su jaki, wannan na ya sanya wata kungiya ta bara, sakamakon yiwuwar bacewar jakuna daga doron kasa, saboda yadda ake cin su a kasar China.

Jaridar BBC ta ruwaito cewa ana kashe miliyoyin jakuna a kasar China, inda ake cin namansa, kuma ake amfani da sauran sassan jikinsu, ciki har da fatar Jakin.

KU KARANTA: NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito har a nahiyar Afirka akwai kasashen dake amfani da jaki, musamman fatarsa, inda aka ruwaito akwai manyan mayankar jakuna guda uku babban birnin kasar Kenya, Nairobi.

Magungunan da fatar Jaki ke yi ga wasu cututtuka da suka addani dan Adam
Jakai

Bincike ya nuna ana amfani da fatar Jaki wajen maganin cutar Daji, sa’annan kuma fatar Jaki na yin maganin Tsufa, fatar Jaki na yin wannan maganin ne bayan dafa shi, inda hakan ke samar da wani sinadari, da aka fi sani da suna (Gelitine).

Magungunan da fatar Jaki ke yi ga wasu cututtuka da suka addabi dan Adam
Fatar Jaki

A wani hannun kuma an bayyana sinadarin a matsayin wani magani dake rage ma mata matsalar da suke fuskanta da zarar sun daina haila. Bugu da kari Sinadarin na magance matsalar barci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng