Yar Sarkin Kano Gimbiya Siddika ta haifi danta na fari tare da mijinta (hotuna)
Ya karade shafukan zumunta cewa yar sarkin Kano, gimbiya Siddika Sanusi-Umar ta samu karuwa inda ta haifi danta na fari tare da maigidanta.
An gano sarki Sanusi Lamido Sanusi dauke da jikansa. Sabon jaririn da aka haifa ya fito shar da shi.
Kwanakin baya, mahaifiyar yaron ta yi kasu kyawawan hotuna da tsohon cikin yaron. Tayi kyau sosai cikin doguwar riga wanda ya dace da jikinta.
Idan zaku tuna Fulani Siddika Sanusi ta auri masoyinta, Abubakar Umar Kurfi a ranar 23 ga watan Disamban 2016. An gudanar da bikin auren a fadar sarkin Kano.
KU KARANTA KUMA: Buhari na kewaye da mutane dake jan kambun mulki domin ra’ayin kansu – Shehu Sani
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng