Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam

Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam

Bawon ayaba yana kunshe da arziki na sunadaran gina jiki (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki (carbohydrates). Akwai ire-iren sunadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wadanda suke da alfanu daban-daban ga lafiyar jikin dan Adam.

Ga jerin hanyoyi 10 da bawon ayaba ke inganta lafiyar jikin dan Adam.

1. Hasken hakori

Goga bawon ayaba ga hakora sau daya a kullum har na tsawon sati guda ko da kuwa na minti guda ne, yana matukar kalkale hakora su fita tar kamar haksen walkiya.

2. Fitar da tusar jaki

Mulka bawon ayaba yana taimakawa wajen ficewar tusar jaki da kuma hana bayyanar wat sabuwa a jikin dan Adam

Amfani 9 na bawon ayaba ga rayuwar Dan Adam
Amfani 9 na bawon ayaba ga rayuwar Dan Adam

3. A matsayin ci ma.

Ana amfani da bawon ayaba a matsayin abin ci, domin kuwa mutanen kasar Indiya sun gano cewar sanyawa dahuwar kaza bawon ayaba yana kara laushin tsokar ta kaza.

4. Waraka ga kurajen fuska

Goga bawon ayaba ga kurajen fuska cikin minti 5 har na tsawon mako guda za a sha mamaki.

5. Rage yakunewar fata

Hada bawon ayaba tare da kwanduwar kwai kuma a shafa ga fuska sannan a wanke da ruwa, ya na matukar warware fata ta yi luwai-luwai.

KARANTA KUMA: Shekaru 57 da samun 'yancin kai: Jerin shugabannin kasa da Najeriya ta yi

6. Sauki ga buguwa a jiki

Shafa bawon ayaba ga wata buguwa ko wani ciwo na jiki yana taimakawa wajen rage radadin ciwon cikin gaggawa.

7. Waraka ga cutar makero

Bawon ayaba ya na taimakawa wajen kawar da cutar makero wadda turawa suke kiranta da Psoriasis. Ya na kuma taimakawa wajen rage radadin kaikayi na makeron

8. Cizon kwaruka

Shafa bawon ayaba akan cizo kamar na sauro yana dauke kaikayin zafin cizon

9. Kyalkyali

Goga bawon ayaba ga fatar takalmi, jakar leda ko azurfa yana sanya su zamto cikin kyalkyali a koda yaushe.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng