Mu leƙa Kannywood: Ciwon dake damun jarumin Fim ɗin Hausa Warangis yayi kamari
Shahararren dan Fim din Hausa mai suna Warangis na cigaba da fama da cutar koda, kuma a hanzu haka zutar tayi kamari a tattare da shi, inji rahoton jaridar Rariya.
Sai dai har yanzu, duk da halin da Warangs ke ciki, babu wani dan Fim daya yi yunkurin taimaka ma jarumin don a yi masa wankin koda in banda wasu yan kalilan, kamar yadda Ibrahim Warangis, yaronsa ya shaida ma majiyar Legit.ng.
KU KARANTA: Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi
Ibrahim, wanda shine yaro daya tilo da Allah ya baiwa majinyacin, yace “Mahaifina na fama da jinya sosai, sai dai babu wani mai bamu taimako, har da masana’antar Kannywood kuwa.”
Ibrahim ya kara da cewa a yanzu haka ciwon mahaifinsa ya kai matsayin a yi masa wankin koda. Amma Ibrahim din yace a kwanaki Ali Nuhu ya basu N25,000, yayin da Sadik Sani ya basu N35,000, bayansu babu wanda ya taimake su a cikin yan Fim.
Daga bangaren sauran jama’a kuwa, Ibrahim yace Hajiya Zainab Ziya’u ta basu taimakon N220,000, sai kuma kanwar Ummi Zee Zee, Haseena data basu N300,000, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng