Dandalin Kannywood: Fati Muhammad ta shiga siyasa tsundum
Shahararriya, fitacciya kuma tsohuwar jarumar fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Fati Muhammad fa ta shiga harkokin siyasa tsundum yayin da yanzu aka soma kada gangar siyasar zabuka masu zuwa na 2019.
Yanzu haka dai jarumar kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu ita ce ke matsayin Daraktar mata ta wata gidauniyar tallafawa al'umma karkashin kulawar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar reshen arewa maso yamma.
KU KARANTA: Yan fim suma 'ya'ya ne kamar kowa - Saima Muhammad
Legit.ng dai ta samu cewa kafin ta samu wannan karin matsayin Fati Muhammad a da ita ce Daraktar mata na gudauniyar amma reshen jihar Kaduna kadai.
Yanzu dai jihohin da tsohuwar jarumar za ta jagoranta sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Jigawa da Zamfara.
Gidauniyar ta Atiku an kafa ta ne kacokan don ta rika tallafawa marasa karfi, wadanda suka hada da talakawa, marayu, yan gudun hijira da sauransu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng