Mawakan Duniya 3 da su ka fi kowa samun kudi a bana
– Mun kawo jerin Mawakan da su ka fi kowa hada kudi a Duniya
– Jerin na dauke da kudin da ‘Yan wasan su ka samu ne a bana
– A wannan shekarar babu wanda ya samu kudi irin P-Diddy
Idan kun a tare da mu kamar yadda aka saba a kowace shekarar Mujallar nan ta Forbes kan fito da sunayen wadanda su ka fi kowa samun kudi a kowace shekara. A bana dai shararren Mawakin nan P-Diddy ne a gaba yayin da irin su Dr. Dre su ka ja baya.
1. P-Diddy
Sean Combs ko kuma kace Puf Diddy kamar yadda aka san shi ya fi kowa samun kudi cikin Mawakan Duniya a shekarar nan da akalla Dala Miliyan $130.
KU KARANTA: Tsohon Dan wasan Najeriya ya bar tarihi a Ingila
2. Drake
Wanda ya zo na biyu a sahun dai shi ne Mawakin nan Drake ‘Dan asalin Kasar Kanada wanda a bana ya kece raini kwarai da gaske inda ya hada kusa da Dala Miliyan $100.
3. Jay – Z
Daga nan kuma sai Babban Mawakin nan Jay-Z wanda a bana ya samu sama da Dala Miliyan $40 Inji Mujallar Forbes.
Irin su Kendrick Lamar dai ba su cikin sahu na 5 din farko ko da ya samu abin da ya kai Dala Miliyan 30 a bana. Fitattun Mawaka irin su Nicki Minaj, Lil –Wayne da DJ Khalid dai su na cikin sahun Mawaka 20 da su ka samu kudi a shekarar ta 2017.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng