Dandalin Kannywood: Yan matan fim 'ya'ya ne kamar naku da kuka killace a gida - Saima Muhammad

Dandalin Kannywood: Yan matan fim 'ya'ya ne kamar naku da kuka killace a gida - Saima Muhammad

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywwod Saima Muhammad ta fito ta shaidawa da duniya a wani irin salo na maida martani da babbar murya cewar su ma fa 'ya 'yane kamar dukkan sauran mata.

Fitacciyar jarumar tayi wannan kalaman ne a yayin wani taron da fitattun matan fim din suka shirya da zummar kafa kungiyar su a wani dakin taro dake a cikin garin Kano.

Dandalin Kannywood: Yan matan fim 'ya'ya ne kamar naku da kuka killace a gida - Saima Muhammad
Dandalin Kannywood: Yan matan fim 'ya'ya ne kamar naku da kuka killace a gida - Saima Muhammad

KU KARANTA: An kamma jigilar alhazan Najeriya daga Makka

Legit.ng ta samu dai cewa Saima Muhammad dake jagorantar tafiyar ta kungiyar ta fada a cikin jawabin nata cewa makasudin kafa wannan kungiyar tasu shine domin fadakar da al'umma irin darajar da matan fim suke da ita kamar sauran mata.

A cewar ta: "Mu ma mata ne masu daraja da kima tamkar wadan da iyayen su ke killace su ko kuma su kaisu kasashen waje yin karatu."

Ta cigaba da ciwa daga cikin manufofin kungiyar ta su za su rika kai ziyara asibiti tare kuma da taimakwa marasa lafiya da sauran marasa galihu a cikin al'umma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng