Gwamnati za ta canza sunayen Masarautun Jihar Kaduna

Gwamnati za ta canza sunayen Masarautun Jihar Kaduna

- Gwamnatin Kaduna za ta sakewa wasu Masarautun ta suna

- Masarautun Kudancin Jihar da kuma tsakiya ne za a taba

- Dama dai a baya Gwamnati ta rage wasu Masarautun

Jaridar Daily Trust na kasar nan ta ce ta fahimci cewa Gwamnatin Jihar Kaduna za ta sakewa wasu Masarautu suna a fadin Jihar.

Gwamnati za ta canza sunayen Masarautun Jihar Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna

Labari ya iso mana cewa za a canza sunayen wasu Masarautu da ke tsakiyar Jihar Kaduna da kuma Kudancin Kasar har kusan 13. Tuni ma dai an nada wani kwamitin mutane 13 da za su yi wannan aikin cikin watanni 6.

KU KARANTA: Yadda mu kayi da Buhari game da 2019 - Inji El-Rufai

A baya dai Gwamnatin Nasir El-Rufai ta sauke wasu Dagatai da Lawanan Unguwanni rututu saboda rage kashe kudin Gwamnati wanda tuni wasu masu sarautar su ka garzaya Kotu. Babu dai Sarkin da aka taba a Kasar cikin guda 32 da ake da su.

Kwamishinan harkar kananan Hukumomi da wasu Jami’an Gwamnati ne da wasu Sarakunan da ma 'Yan Boko a cikin wannan kwamiti. Kuma dai garambawul din da za ayi wanna karo ba zai shafe manyan Sarakunan kasar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Boko Haram sun sace mijin wata mata

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: