Birnin Legas ne na 3 a duniya wajen wahalar tuki, inji wani sabon bincike, duba suwaye cikin jerin
- Legas ne birni mafi jama'a a Najeriya, da ababen hawa, ga rashin fadin kasa
- Forbes Magazine ita ta wallafa rahoton
- Karachi ta Pakistan da Lahore a Indiya sune kan gaba a duniya
A sabon bincike da hamshakiyar jaridar Forbes ta fitar, ta nuna birnin Legas ne na uku a rashin dadin tuki, da ma hargitsi da rashin tsari a duk duniya. Hadari ga matuka da masu aiki a kan titi na karuwa daga birni zuwa birni.
A binciken. birnin Lahore na Indiya, shi ya zoo na daya wajen rashi dadin tuki, hadari da cunkoso, sabili da rashin tsari, inda birnin Karachi na kasar Pakistan yazo na biyu. Hakan zai hana masu son yawon bude idanu ziyartar irin wadannan wurare.
Hakan na nufin wadannan kasashe bassu da cikakken tsari na amfani da ababen hawa, kuma babu doka. Idan ma kuma akwai ta, to cin hanci yayi katutu ya hana a bi tsarin yadda komai zai tai daidai.
DUBA WANNAN: 2019: 'Shugaba Buhari ne zai lashe zabe idan anyi'
A binciken dai, an nuna rashin tsari kan hana motoci gudu sosai, wanda ke bata wa jama'a lokaci, hakan kuma asara ce babba ta kudi idan aka yi la'akari da cewa kudi sune lokaci, kuma lokaci shine ke zama kudi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng