Najeriya ta zama ta biyu a duniya a fannin noman dawa
- Najeriya ta zamo ta biyu cikin kasashen dake noman dawa a fadin duniya
- Kasar Najeriya zata samar da 6.4 cikin metrik tan miliyan 59.34 da za'a samar a 2018 a fadin duniya
- Dawa dai na daya daga cikin abubuwa da ake noman su sosai a Arewacin Najeriya
Rahotanni sun kawo cewa Najeriya ta zamo ta biyu cikin kasashen dake noman dawa a fadin duniya, bayan kasar Amurka, wacce it ace ta daya.
Hasashen adadin dawar da za a noma a fadin duniya a tsakanin wannan shekara da 2018 ya kai metrik tan miliyan 59.34 wanda a ciki kasar Amurka za ta samar da 8.4, yayin da Najeriya da za ta samar da 6.4, inji rahotan.
Sai Mexico, wacce itace kasa ta uku a jerin kashen da ke noman dawan, da ita kuma za ta samar da metrik tan miliyan 6.0.
Daya daga cikin manyan kamfanonin dake amfani da dawa a Najeriya, ‘Nigerian Breweries PLC ta sanar da cewa masana’natu sun yi amfani da akalla kaso 20% na adadin dawar da aka noma a kasar a shekarar 2015, yayin da aka yi amfani da kaso 80 a matsayin abincin mutane da na dabbobi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna Fayose ya kaddamar da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019 a Abuja
Kamfanin ta ce a kowacce shekara, yana amfani da kimanin metrik tan 100,000 na adadin dawar da ake nomawa a Najeriya.
Dawa dai na daya daga cikin abubuwa da ake noman su sosai a Arewacin Najeriya.
A ‘yan shekarun bayan nan, ta zama daya daga cikin manyan kayan hadi da masana’antu musamman na bangaren abinci da kayyakin sha ke amfani da su, duba da irin tarin alfanun da ta kunsa.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng